Jami’an tsaro a birnin Abuja, sun yi arangama da masu zanga-zangar EndSARS, lamarin da ya janyo tsare wasu daga cikin su.

Masu zanga-zangar da su ka taru a harabar majalisar wakilai dai su na neman hukumomi su yi garambawul ga tsarin aikin ‘yan sanda, sakamakon zargin da ake yi masu na zaluntar jama’a.

Rahotanni sun ruwaito cewa, jami’an ‘yan sandan sun rika yin harbi a sama da nufin tarwatsa gungun masu zanga-zangar.

Wata majiya ta ce, shugaban jaridar Sahara Reporters Omoyele Sowere ne ya jagoranci zanga-zangar, wadda ta haifar da cunkoson ababen hawa a titin Shehu Shagari da ke birnin Abuja.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *