Wata Babbar Kotun a jihar Kaduna, ta tabatar da naɗin Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau na 19.

Idan dai ba a manta ba, a watan Oktoba Alhaji Bashari Aminu (Iyan Zazzau) ya shigar da ƙara a Babbar Kotun jihar Kaduna da ke Dogarawa Sabon Garin Zariya, inda ya ke ƙalubalantar naɗin Ahmed Nuhu Bamalli a matayin Sarkin Zazzau.

Sai dai kotun ta yi watsi da ƙarar, inda alƙalin kotun ya zartar da hukuncin cewa za a iya bikin naɗin sabon Sarkin a ranar Litinin 9 ga watan Nuwamba.

Alhaji Bashari Aminu (Iyan Zazzau) dai ya na daga cikin mutanen da su ka nemi sarautar ta Zazzau.

A ƙarar da ya shigar, Iyan Zazzau ya nemi kotu ta tabbatar da shi a matsayin sabon Sarkin Zazzau, kasancewar ya fi samun yawan kuri’un masu zaɓen sabon sarki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *