Jami’an Hukumar Kiyayye Hadurra ta Kasa za su fara amfani da bindiga domin kare kan su daga sharrin masu amfani da tituna a Nijeriya.

Shugaban kwamitin kiyaye hadura na majalisar wakilai Akinfolarin Mayowa ya sanar da haka, yayin kare kasafin hukumar na shekara ta 2021 a Abuja.

Akinfolarin ya yi bayanin cewa, dokar hukumar ta ba jami’an ta ikon rike bindiga.

Ya ce ya zama dole a aiwatar da dokar domin tabbatar da masu amfani da titi su na bin dokoki a kuma inganta aikin jami’an hukumar.

A cewar sa, kare haddura nauyi ne da ya rataya a wuyan duk ‘yan Nijeriya, don haka ya kamata a dauki duk matakan da su ka dace don cimma wannan kudiri.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *