Sakataren din-din-din na fadar shugaban kasa Tijjani Umar, ya ce Naira biliyan 1 da miliyan 300 da aka tanadar wa asibitin fadar shugaban kasa a kasafin shekara ta 2021 ya yi kadan.

Tjjani Umar, ya bayyana wa manema labarai haka ne bayan kare kasafin shekara ta 2021 da ma’aikatar sa ta gabatar a gaban kwamitin harkokin gwamnati.

Umar ya yi alkawarin cewa, shugaban kasa da iyalan sa da manyan jami’an gwamnati sun samu isasshen kayan kula da lafiya idan aka amince da kudin.

Ya ce naira biliyan 1 da miliyan 300 sun yi kadan idan ka hada da kudin da su ka bukata, kuma idan aka kwatanta da asibitocin duniya za a ga cewa kudi ba su yi ko kusa da abin da su ke bukata ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *