Shugaban alƙalan Nijeriya Tanko Muhammad, ya rsantsar da sabbin alƙalai takwas na kotun ƙoli, abin da ya ƙara yawan su zuwa 20 daga 12.

Alƙalan da aka rantsar sun hada da Lawal Garba daga shiyyar Arewa maso yamma, da M M Saulawa daga shiyyar Arewa maso yamma, da Helen Ogunwumju daga shiyyar kudu maso yamma, da Abdu Aboki daga shiyyar Arewa maso yamma.

Sauran sun hada da Adamu Jauru daga yankin Arewa maso gabas, da Samuel Oseji daga kudu maso kudu, da Tijjani Abdulkadir daga Arewa maso gabas, da kuma Emmanuel Agim daga kudu maso kudu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *