Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta rufe dukkanin sansanonin ‘yan gudun hijira dake fadin jihar inda ta maida mutanen zuwa garuruwansu na asali.

Kwamishinan kula da harkokin matasa da ci gaban al’umma, Sani Danlami, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar.

Ya ce sansanonin da aka rufe sun hada da na Dandume, da Faskari, da Kankara, Jibia, Batsari, ATC Katsina da kuma gidajen marasa galihu na jihar.

Ya ce gwamnatin jihar ta dauki wannan mataki ne sakamakon yadda zaman lafiya da tsaro ke ci gaba da komowa a wadannan yankuna da kuma jihar baki daya.

Danlami ya ce gwamnatin jihar ba za ta lamunci duk wani mutum ko al’umma da za su rika yawo a hanyoyi da sunan cewa su ‘yan gudun hijira ne ba.

Sannan ya ba ‘yan jihar tabbacin cewa gwamnati ba za ta nade hannu tana kallon wasu na bata mata suna a idon duniya ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *