Kwamitin da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa domin bincike kan zargin jami’an ‘yan sanda da cin zarafin al’umma ya bukaci ‘yan jihar da su gabatar da korafe-korafen su.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun sakatariyar kwamitin Hajara Jibrin Abubakar.

Ta ce ana shawartan duk wanda yake da korafi da ya shafi cin zarafi daga rundunar ‘yan sanda ya gabatar da korafe-korafensa kafin ranar 25 ga wannan watan.

Hajara ta ce za a gabatar da korafe-korafen ne a rubuce, sannan a rubuta zawa ga ofishin sakatariyar kwamitin da gwamnatin ta kafa domin bincike.

Ta ce akwai bukatar ko wani korafi ya taho da shaidu dake tabbatar da hakan, da suka hada da hotuna, bodiyo, da sauran wasu shaidu dake hannu.

Ta kara da cewa akwai bukatar ko wani korafi ya kunshi sunan mai gabatarwa, lambar waya, adireshi wanda hakan zai bada damar nemansa ya bada shaida a fili.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *