Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce za ta fara yin rijistar masu kada kuri’a a watanni huddun farkon shekarar mai zuwa.

Shugaban hukumar na kasa Mahmood Yakubu, ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, jim kadan bayan ya bayyana a gaban kwamitin kula da harkokin zabe na majalisar dattawa domin kare kasafin hukumar na shekarar 2021.

Ya ce za a gudanar da aikin yin rijistar masu kada kuri’ar ne na tsawon watanni 6 kafin zaben shekarar 2023.

Ya ce yanzu haka hukumar na kare kanta a kotu kan wasu kararraki dubu 1 da dari 7, da wasu suka shigar gabanni da kuma bayan zaben shekarar 2019.

Yakubu ya ce hukumar ta cimma matsaya kan cire sama da billiyan 5 daga cikin kudaden ta billiyan 10 domin cike gibin kasafin wannan shekarar na hukumar.

Ya ce hukumar ba ta taba cire kudaden na asusun bat un daga shekarar 2010, kuma a tsari za a rika taba kudaden ne lokaci zuwa lokaci idan bukatar hakan ta taso.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *