Hukumar kula da albarkatun man fetur DPR ta gargadi masu saida iskar gas dake amfani da hanyar tunkunya da tukunya, wanda a cewar ta hakan na da hadarin gaske.

Babban jami’in hukumar dake kula da shiyyar Yola, Sadiq Ibrahim ya bayyana haka a lokacin gudanar da wani taron wayar da kai da aka shiryawa masu saida iskar gas a jihar.

Ibrahim ya ce gargadin ya zama wajibi domin kare iftila’in gobara da kuma tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma.

Ya ce hukumar ba za ta ci gaba da amincewa masu sai da iskar gas ta hanyar da bata dace ba, domin hakan na tattare da hadarin gaske.

Ibrahim ya kara da cewa hukumar ta karbi rahoton tashin gobara a wurare daban-daban dake fadin kasar nan, sakamakon yin sana’ar ba bisa ka’ida ba.

Sannan ya shawarci masu sana’ar da su kara koyon hanyoyin da suka kamata subi domin kare kawunansu da kuma al’umma baki daya, domin a cewarsa hukumar ba ta adawa da sana’ar tasu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *