Gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i sun gaza cimma matsaya kan bukatun da kungiyar ta gabatarwa gwamnati kafin ta dakatar da yajin aikin da ta shiga.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Chris Ngige ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala ganawar sirri tsakanin tawagar gwamnati da shugabannin kungiyar ta ASUU.

Daga cikin bukatun da kungiyar ta gabatar har da cika alkawari kan basu wasu kudade kamar yadda aka cimma yarjejeniya tsakanin kungiyar da gwamnati a shekarar 2009.

Ministan ya ce ba wai gwamnati ba ta son biyan kudaden bane, halin da ake ciki na matsalar tattalin arziki sakamakon bullar cutar korona ya sa ba za ta iya ba bangaren kudaden a yanzu ba.

Ya ce abubuwan da ake bukata shine tabbatar da gaskiya da adalci a dukkanin jami’o’i dake fadin kasar nan, tare da tabbatar da cewa ana yin komai a fili.

A cewarsa kungiyar ta nuna adawa da amfani da tsarin biyan albashi na IPPS, duk da cewa shine kadai tsarin da gwamnatin ta amince ayi amfani dashi wajen biyan albashin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *