Kamar yadda muka ce wasu na ganin ga dukkan alamu jawabin da Joe Biden ya fito ya yi ya zaburo shi ya aiko sako a shafinsa na tiwota tare da cewa shima zai yi bayani nan da dan lokaci kadan.

To ya kuwa yi bayanin inda ya ayyana a gaban jama’a cewa shi ne ya yi nasarar lashe zaben Amurka na shugaban kasa.

Ya kuma kara da cewa ba za au bari a murde musu zaben ba ta hanyar aringizon kuri’u nan da wayewar gari da sunan wai an kada kuri’un ne ta wata hanyar da ba gaskiya bace face magudi.

Sai dai kuma da ya gayyaci mataimakinsa Mike Pence don ya ce wani abu, sai kawai mataimakin yayi masa abin nan da ake cewa naka ahi ke bada kai. 

Inda Mike cikin natsuwa yace, zamu sa ido kar don kar a mana aringizo a cikin kidayar kuri’un da a ke yi. Mataimakin nasa da ake kallo a matsayin ya fishi taka-tsantsan bai yarda ya furta cewa sun ci zabe ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *