A yau ne a ke ci gaba da kada kuri’ar zaben shugaban kasar Amurka na shekara ta 2020 bayan gama wa’adin farko na mulkin shugaba Donald Trump. 

Fafatawar da ke gudana tsakanin shugaban kasar Donald Trump mai ci na jam’iyyar ‘Republican’ da kuma Joe Biden dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta ‘Democrat’ kuma tsohon mataimakin shugaban Amurka karkashin mulkin Barack Obama. 

Yanzu haka dai an fara samun wasu jihohin da suka fara fitar da sakamakon zabensu har ma wasu rahotanni na nuna Biden na kan gana da kuri’u 192 daga cikin 270 da yake nema a yawan jihohin raba gardamar masu nauyi nan da a turance suke kira da ‘electoral votes’ shi kuma Trump yana biye da kuri’u 108 a jihohin.

Amma komai na iya faruwa tunda har yanzu ana ci gaba da bayyano sakamakon wasu jihohin a daidai lokacin da muke rubuta wannan rahoto karfe 11 na dare a Washington da ke gundumar Columbia.

Tuni dai wasu makwannin da suka shude Amurkawa ke ta kada kuri’arsu daga gida ta hanyar aika zabinsu ta akwatin gidan waya. Har kuma zuwa wannan rana ta 3 ga Nuwambar an sami sama da mutum miliyan dari da suka yi zaben wuri.

A ranar 2 ga watan zaben ne dai ‘yan takarar suka karkare yakin neman zaben a wasu daga jihohin da ke da karfin masu zabe irin su Pennsylvania da kakkausan lafazai. Inda Joe Biden ya ce lokaci yayi da shigaba Trump zai tattara komatsansa ya nufi gida domin Amurkawa sun gaji da yarfa su da shugaban yake a idon duniya.

Shi kuwa a martanin Trump cewa ya yi yana kira ga Amurkawa da su yi zaben na gari kamarsa da zai bunkasa musu yalwa da tattalin arziki ba irin Joe sarkin barci ba. Haka kuma ya musanta cewa wai zai ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zabe tun kafin a fadi sakamako.

Amma ya tabbatar da cewa matukar aka ci gaba da kidayar kuri’u fiye da ranar zaben, to kuwa zai kalubalanci abin a kotu. Duk da yake dai a jiya ma’abocin aika sakonnin tiwitar ya rubuta wani sako da ya nuna cewa a guji yin magu-magu a zaben don kar a tunzura mutane su fantsamq kan tituna bisa rashin amince wa. 

To sai dai tuntuni kamfanin tiwita ya yi waje wannan rubutu daga kan shafin na Trump da jama’a ke kallo a matsayin filin dagarsa da ya ke taka duk wanda ya ga dama da sunan ‘yancin fadin albarkacin baki.

Duk ‘yan takarar suna cike da yakinin bawa abokin hamayya mamaki ta hanyar dankara shi da kasa a zaben. Haka kuma bisa yadda wasu ke dar dar din kar abin ya zama rikici, har wasu shaguna kandagarki suka yi wajen manne mashigar shagunansu da fallen katako da karafa.

Yanzu abin jira a gani shine ya za a karkare zabe da yadda sakamako zai kaya zuwa washe gari da kowa ne allazi zai kama nasa amanu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *