Ana cikin samun sakamakon zaben shugaban Amurka na 2020 daga jihohin kasar guda 50, sai babban dan takarar jam’iyyar adawa Joe Boden ya bayyana kan dandali da bayani kamat haka.

“Mu yi ta hakuri magoya baya, don shine ya kamata mu yi domin kuwa ana iya kwana har zuwa gobe ko ma a wuce haka wajen kidayar kuri’unmu. Amma dai haka dama tsarin yake, don haka mu ci gaba da hakuri. Sannan a haka ma mun gamau da rawar da sakamakon zaben ke takawa, kuma muna jiyo kanshin yin nasara.

Musamman akwai kuri’un da aka kada ta gidan waya, don haka zai dauki lokaci ana kirge don haka a ci gaba da hakuri. Mun gode muku kwarai da gaske.

Kuma ba hurumina ko na Donald Trump ba ne ayyana wanda ya yi nasara a zaben nan, amma ina da yakinin sakamakonsa zai mana kyau.”

Haka dai ya ci gaba da bayanin cewa yana sa ran har Pennsylvania za su lashe kawai dai kidayar kuri’a zai iya daukar lokaci. Karshe shi da matarsa da ke kan dandalin sun gode wa masoyansu da jaddada musu batun hakuri da juriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *