Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na 3, ya bukaci gwamnatin tarayya da na jihohi su tabbatar da gaskiya da daidaito ga dukkanin ‘yan Najeriya.

Basaraken wanda shine shugaba majalisar koli kan harkokin addinin Musulunci, ya bayyana hakan ne a wani taron gaggawa da majalisar sarakuna ta kira a Abuja.

Taron wanda yake da nasaba da irin fargabar ballewan rikici a wasu yankunan Najeriya ya maida hankali ne kan hanyoyin da za a bi wajen samar da mafita.

Sultan ya kuma bukaci ‘yan siyasa da su rika sanya muradun kasa a kan gaba kafin duk wasu bukatu nasu.

Sannan ya bada tabbacin cewa a shirye sarakuna suke su hada hannu da sauran hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da ci gaba da zaman lafiya.

A nasa jawabin Oni na Ife Oba Adeyeye Ogunwusi, ya bukaci gwamnatin tarayya ta fito da wasu shirye-shirye da zai sa ta kusanci al’umma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *