Majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Nijeriya, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi gaugawar daukar mataki a kan Fasto Godfrey Igwebuike Onah, biyo bayan hudubar Faston da ta janyo kashe wasu musulmai da ke zaune a kudu maso gabas da kudu maso kudancin Nijeriya.

Haka kuma, majalisa, wadda ke karkashin jagoran Sarkin Musulmi, ta kai korafi ga shugaban ‘yan sandan Nijeriya, da shugaban hukumar tsaro ta DSS Yusuf Magaji Bichi.

Mataimakin sakataren majalisar Farfesa Salisu Shehu, ya na zargin Faston da yin hudubar da ta janyo kashe musulmai tare da barnata dukiyoyin su.

A cikin takardun korafin, Salisu Shehu ya sanar da shugaban ‘yan sandan Nijeriya da na DSS cewa, an kai wa Musulmai hari babu gaira babu dalili a kudancin Nijeriya, inda aka kashe wasu tare da janyo asarar dukiya ta biliyoyin naira.

Ya ce an kona masallatai, daga ciki har da tsofaffin masallatan da asalin musulmin kabilar Ibo su ka gina.

TSARO: MU MASU TSANTSAR BIYAYYA NE GA SHUGABAN KASA – BURATAI

Shugaban rundunar sojin kasa ta Nijeriya Janar Tukur Buratai, ya jaddada biyayyar jami’an rundunar soji ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Buratai ya bayyana matsayin sa ne, yayin da ya ke jawabi a wajen bude taron rundunar sojin Nijeriya na kwanaki biyu a birnin Zaria na jihar Kaduna, inda ya samu wakilcin kwamandan dakarun soji Manjo Janar Stevenson Olabanji.

Ya ce fara da isar da sakon godiya ga shugaba Muhammadu Buhari, sakamakon goyon bayan da ya ke ci-gaba da ba rundunar sojin Nijeriya wajen sauke hakkin da ya rataya a wuyan ta.

Janar Buratai, ya ce ya sha alwashin tabbatar da jajircewa da biyayyar jami’an rundunar sojin Nijeriya ga Shugaba Buhari tare  da kare martabar damokradiyya.

Ya ce ya bada muhimmanci wajen horo tare da sake horar da jami’an rundunar sojin domin aiwatar da ayyukan su yadda ya kamata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *