Kwamin kula da harkokin sojin sama na majalisar wakilai ya yabawa shugaban rundunar sojin saman Najeriya Air Vice Marshal, Sadiq Abubakar bisa namijin kokarin da yake na magance matsalolin tsaro a fadin kasar nan.

‘Yan majalisun sun bayyana hakan ne a lokacin da suka kai ziyarar gani da ido shelkwatar rundunar sojin dake Abuja.

Shugaban kwamitin Shehu Koko, ya yaba da irin aiki da shirye-shirye da rundunar sojin saman key i, musamman wajen samar da kayayyakin aiki da dabarun yaki.

Ya ce kwamitin zai ci gaba da yin dukkanin mai yiwuwa wajen marawa rundunar sojin baya, musamman kan kokarin yaki da ‘yan ta’adda da suka addabi Najeriya.

A nasa jawabin mai magana da yawun majalisar ta wakilai Benjamin Kalu, ya ce bai zama wajibi ‘yan Najeriya su ankara akan irin namijin kokari da rundunar sojin ke yi ba, amma an samu nasarori sosai.

Shima shugaban rundunar sojin Sadiq Abubakar, ya nuna godiyarsa ga kwamitin, tare da yin kira gare su da su cewa rundunar na da bukatar karin kudi a kasafin kudi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *