Wata kotu a jihar Kano ta soke belin da aka ba fitaccen mawaƙin nan Naziru Ahmed, inda ta gindaya wasu sababbin sharuɗɗan belin.

Kotun ta tura Naziru gidan yari saboda rashin cika sharuɗɗan a kan lokaci.

Ana ƙarar Naziru ne kan wata waƙa da ya sake ba tare da hukumar tace fina-finai ta Kano ta tantance ba.

Sharuɗɗan belin sun haɗa kawo wani Maigari da zai tsaya masa da kuma Kwamandan Hizbah na ƙaramar hukuma.

Wani na hannun daman ya ce sun cika sharuɗɗan, sai dai kuma ba a samu kai wa ga alƙalin da zai bayar da umarnin ba da belin ba.

A watan Satumban 2019 ne aka fara kama Naziru amma daga bisani kotun majistare ta sake shi bayan ya cika sharudan belin da kotun ta gindaya masa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *