Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa da amincewar ta ne Sojin Amurka suka shigo domin ceto wasu mutanan su da aka yi garkuwa da su a karshen makon nan.

Ministan tsaro, Bashir Magashi ya bayyana haka inda yake cewa Najeriya tana sane kuma da amincewar ta ne sojin Amurkan suka shigo domin kaddamar da aikin.

Bashir Magashi, ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake amsa wata tambaya bayan da ya gama kare kasafin kudin ma’aikatar sa ta tsaro na shekarar 2021 a gaban kwamitin majalisar Dattawa a nan Abuja.

Gwamnatin ta tarayya ta ce ko kusa aikin da Sojin musamman na kasar Amurka su ka shigo suka yi a cikin Najeriya ba kutse ne suka yi ba.

Akwai dai masu rade-radin cewa aikin ceton da Sojin musamman na kasar ta Amurka suka shigo suka yi keta hurumin Najeriya ne.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *