Shugaban karamar hukumar Nsukka Ngwueze, ya ce gwamnatin jihar Enugu ta yi alhinin yadda bata-gari su ka rushe masallatai biyu da ke karamar hukumar sa, ya na mai bada tabbacin cewa za a fara aikin kara gina masallatan da aka rushe.

Yayin da ya ziyarci yankin da lamarin ya shafa, Ngwueze ya ce ya je ne don ya tabbatar wa mutanen Enugu cewa gwamnati za ta biya duk wanda asara ta same shi sakamakon zanga-zangar EndSARS.

Ya kuma yaba wa shugabannin musulmai a kan hakurin da su ka yi a lokacin da rigimar ta hargitse a jihar.

Ya ce ya yaba wa shugabannin musulmai a kan yadda su ka kwantar da hankulan su ba su kuma kai wa kowa farmaki bayan rushe masallatan da aka yi masu ba.

Limamin babban masallacin Nsukka Yakubu Omeh, ya yi godiya ga shugaban karamar hukumar a kan ziyarar da ya kai masu, inda ya tabbatar da alkawarin gwamna a kan kara gina masallatan da ya yi.

Gwamnan jihar Enugu Ifeanyi Ugwuanyi dai ya umarci a kara gina masallatai biyu da masu zanga-zanga su ka rushe.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *