Ministar kudi Zainab Ahmed, ta ce tulin bashin da ke kan Nijeriya zai kai naira tiriliyan 38 da biliyan 68 nan da watan Disamba na shekara ta 2021.

Zainab ta yi kintacen ne a gaban Kwamitin Bin Biddigin Basussukan Cikin Gida da na Waje da ake bin Najeriya a zauren Majalisar Dattawa.

An dai gayyaci ministar ne domin yi wa kwamitin karin haske dangane da tulin bashin da ake bin Gwamnatin Tarayya da Jihohi 36 har da birnin tarayya Abuja, biyo bayan yawan damuwar da ake nunawa dangane da yawan tulin basussukan.

Gwamnatin shugaba Buhari dai ta shirya ciwo bashin naira tiriliyan 4 da biliyan 28, domin cike gibin kasafin shekara ta 2021 saboda rashin isassun kudade.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *