An fitar da wata sanarwa mai kunshe da ranar da za a yi bikin nadin sarautar sabon sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli.

A ranar Litinin da ta gabata ne, shugabanni kwamitin shirye-shiryen nadin sarautar Zazzau su ka sanar da Litinin, 19 ga watan Nuwamba na 2020 a matsayin ranar da za a yi bikin nadin.

Sanarwar ta ce, za a yi nadin ne a filin wasan Polo da ke sabon gari Zaria, sannan an sanar da Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai cewa shi ne babban bako a wajen nadin.

Haka kuma, akwai manyan baki da ake sa ran za su halarci bikin, wadanda su ka hada da ministoci da ‘yan majalisar dokoki ta jiha da manyan ‘yan siyasa da manyan ‘yan kasuwa da manyan ma’aikatan gwamnati da ke fadin Nijeriya.

TA’ADDANCI: ‘YAN BINDIGA SUN KASHE MATA MAI JUNA BIYU SUN YI GARKUWA DA MIJIN TA A KADUNA

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun kashe wata mata mai juna biyu a unguwar Rigachikun da ke garin Kaduna.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun sace matar ne tare da mijin ta daga gidan su, amma sun kashe matar yayin da su ke musayar wuta da jami’an tsaro da ke ƙoƙarin ceto wadanda abin ya faru da su.

Har yanzu dai ba a gama samun cikakken bayani a kan afkuwar lamarin ba.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna ASP Muhammad Jalige bai riga ya amsa tambayar da aka yi ma shi game da lamarin ba, amma majiyar ta ce masu garkuwar sun afka gidan wadanda abin ya faru da su ne su ka yi awon gaba da su, daga nan jami’an tsaro su ka bi sawun su, inda yayin musayar wuta masu garkuwar su ka harbe matar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *