Shugaban ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya ce rundunar ta kama mutane dubu 1 da dari 5 da 90, da ake zargi na cikin wadanda suka yi zanga-zangar da ta rikide zuwa tashin hankali a wasu jihohin kasar nan.

Adamu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yiwa jami’in ‘yan sanda da manema labarai jawabi a ziyarar gani da ido wuraren da masu zanga-zangar suka kona a Legas.

Shugaban ‘yan sandan ya yabawa jami’an rundunar bisa irin kwarewa da juriya da suka nuna a lokacin da masu zanga-zangar suka wuce gona da iri, ta hanyar kai musu hare-hare.

Adamu ya ce rikicin da kuma asarar da aka tafka a lokacin zanga-zangar ya fi shafar jihohi 14 dake fadin kasar nan, ciki har da Legas dake sahun gaba.

Ya kara da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, na yabawa jami’an ‘yan sandan bisa kokarin da suke na tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *