Hukumar shirya jarabawar kammala makarantar sakandire ta NECO, ta ce za a ci gaba da zana jarabawar da aka dakatar daga ranar 9 ga wannan watan da muke ciki.

Jami’in yada labarai da hulda da jama’a na hukumar Azeez Sani, ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja.

Idan dai za a iya tunawa a ranar 21 ga watan da ya gabata ne shugabannin hukumar suka kira taro na musamman inda suka dakatar da rubuta wasu daga cikin jarabawar a fadin Najeriya.

A kuma ranar 25 ga watan hukumar ta fitar da sanarwar dakatar da rubuta jarabawar har sai illa ma sha Allahu, sakamakon zanga-zangar masu adawa da rundunar SARS.

Hukumar ta kuma yaba tare da yin godiya ga al’ummomi musamman dalibai da suka bata hadin kai kan matakin da ta dauka na dakatar da jarabawar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *