Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bada umurnin zama da masu ruwa da tsaki da suka hada da sarakunan gargajiya, matasa da sauransu a dukkanin shiyoyin siyasa dake fadin kasar nan.

Ministan kula da harkokin yada labarai da al’adu Lai Muhammad, ya bayyana haka jim kadan bayan ganawar sirri da tawagar gwamnatin tarayya ta yi da gwamnonin Arewa 19 a Kaduna.

A cikin kwamitin wanda shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Ibrahim Gambari ya jagoranta, akwai ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammad, Ministan babban birnin tarayya Abuja, Muhammad Bello, da shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu.

Sauran sun hada da shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan, da mataimakin shugaban majalisar wakilai Ahmed Idris Wase, da sauran wasu ‘yan majalisar dokoki.

Lai Muhammad ya ce ganawar za ta maida hankali ne kan hanyoyin samar da ci gaba da hadin kai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *