PIC. 12. HOUSES IN SOME PART OF JIMETA, YOLA NORTH LOCAL GOVERNMENT AREA SUBMERGED BY FLOOD FOLLOWING THE RELEASED OF WATER FROM LAGDO DAM IN THE REPUBLIC OF CAMEROON ON SUNDAY (26/8/12).

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta ce akalla mutane dubu dari da 58 ne ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomi 18 dake jihar Kebbi.

Tawagar hukumar kakkashin jagorancin, jami’in dake kula da shiyyar Sokoto Tukur Abubakar, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Kebbi, jim kadan nayan ganawa da gwamnan jihar.

Tukur ya ce tawagar ta dira a jihar ce tun bayan makwanni 3 da suka gabata, inda ta ziyarci dukkanin wuraren da abin ya shafa domin tattara bayanai.

Sannan ya ba wadanda ambaliyar ta ruwan tabbacin kawo musu daukin kayayyaki, jim kadan bayan kammala tattara bayanan irin barnar da ta yi.

Tukur ya kuma yabawa hukumar bada agajin gaggawa ta jihar bisa hadin kai da goyon bayan da ta bada tare da kaiwa wadanda abin ya shafa tallafin gaggawa.

A nasa jawabin shugaban hukumar bada agajin ta jihar Kebbi Sani Dododo, ya yabawa tawagar bisa ziyarar da ta kai cikin a wannan lokaci da Najeriya ke fuskantar baranar masu zanga-zanga.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *