Kwamitin kula da harkokin wasanni da ci gaban matasa na majalisar wakilai ya sha alwashin bada goyon baya ga shirin ba matasa horo domin zama masu dogaro da kawunansu a fadin Najeriya.

Shugaban kwamitin Yemi Adaramodu, ya bayyana haka a wajen kare kasafin kudin shekarar 2021 na ma’aikatar kula da harkokin wasanni da ci gaban matasa a Abuja.

Ya ce suna tattaunawa da bangarori da masu ruwa da tsaki a ma’aikatu domin tabbatar da cewa an aba matasa damar da ta kamata a basu.

Adaramodu ya nuna damuwa kan kasafin kudin da aka warewa bangaren, wanda a cewarsa akwai bukatar yin wani abu da zai daga darajar matasa a Najeriya.

Ya ce duba da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, kamata ya yi a yiwa bangaren matasa kaso na musamman da ba a taba samun irinsa ba.

A cewarsa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta fito da wasu tsare-tsare da daman a ci gaban matasa, sai dai ya nuna damuwa akan hanyoyin da ake bi wajen kaddamar dasu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *