Kungiyar gwamnonin Arewa ta nuna goyon bayan ta na kokarin da ake wajen sanya dokar shafukkan sada zumunta domin dakile yada labaran karya da ka iya haifar da hatsaniya a fadin Najeriya.

Kungiyar ta bayyana matsayar ta ne a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun shugabanta kuma gwamnan jihar Plateau Simon Lalong, jim kadan bayan ganawa da masu ruwa da tsaki a Kaduna.

Ganawar ta maida hankali ne kan hanyoyin da za a bi wajen magance yadda ake amfani da shafukkan sada zumunta wajen yada labaran kanzon kurege.

Kungiyar ta kuma nuna goyon bayan ta ga shirin sake fasalin rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta yadda za a sake samun kwarewa da ci gaba a bangaren.

Kungiyar ta kafa wasu kwamitoci biyu na musamman da za su maida hankali wajen tattaunawa da sarakunan gargajiya, matasa da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da mafita.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *