Gwamnatin tarayya ta ce an samu jinkirin biyan albashin watan Oktoba ne sakamakon amincewa da kasafin kudin wannan shekarar a lokacin da ba a cimma matsaya kan sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikata ba.

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya Folasade Yemi-Esan ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun jami’ar yada labarai da hulda da jama’a na ofishin Olawunmi Ogunmosunle.

Ta ce wannan ya tilastawa gwamnatin tarayya yin wasu ‘yan gyare-gyare ta yadda za ta iya biyan sabon tsarin albashin ba tare da an samu matsala ba.

Yemi-Esan ta ce akwai kwamiti na musamman da aka kafa da ya kunshi mutane daga ma’aikatar kasafi da tsare-tsare da kuma ofishin akanta janar na tarayya inda za su gudanar da aiki tare da lalubo hanyoyin magance duk wasu matsaloli da suka kunno.

Yayin da take yabawa ma’aikata, Yemi-Esan ta ce ta yi magana da babban jami’in kula da sashen kasafi, kuma ya bada tabbacin za a biya kafin karshen wannan makon.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *