Shugaban hukumar kula da ‘yan Najeriya dake kasashen ketare Abike Dabiri Erewa, ta ce kasar Egypt za ta maido da wasu ‘yan Najeriya 7 a cikin mutane 8 da suka gudanar da zanga-zangar adawa da rundunar SARS a kasar. 

Dabiri-Erewa ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin ta na twitter.

Ta ce mutanen sun janyo hankalin hukumar kan matakin da kasar ta Egypt ta dauka, na kamasu inda suka bukaci ta shiga tsakani domin barinsu a kasar.

Kasar ta Egypt ta ce za ta maido da mutanen gida Najeriya ne bayan zanga-zangar da suka yi, duk kuwa da cewa basu da visa da kuma izinin zama a kasar.

Mutum guda daga cikin mutanen da za a barshi a kasar shine wanda ya cika ka’idoji, kuma ya dauki alkawarin ba zai gudanar da wani abu da ya shafi dokar kasar.

Idan zai a iya tunawa a watan da ya gabata ne hukumomi a kasar ta Egypt suka kama wasu ‘yan Najeriya a Cairo, biyo bayan zanga-zangar adawa a rundunar SARS.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *