Gwamnonin jihohin arewacin Nijeriya 19, sun taru a Kaduna domin tattaunawa game da matsalar tsaro da ta addabi yankin.

Waɗanda su ka halarci taron sun haɗa da sarakunan gargajiya da shugaban ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Ibrahim Gambari.

Sauran sun hada da Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed, da Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan da ‘yan majalisar wakilai da sauran manyan ‘yan siyasa.

An dai gudanar da taron ne a asirce a ɗakin taro na gidan gwamnatin Jihar Kaduna, inda mai masaukin baki gwamna Nasir El-rufa’I ya fara da cewa, suna fatan tattaunawar ta kasance kan tasirin abubuwan da su ka faru a baya-bayan nan a yankin arewa, da kuma abin da za su iya yi domin rage girman asara da kuma kyautata tsaro ga al’ummar su.

Mahalarta taron sun tattauna a kan abin da ya shafi matsalolin tsaro da zaman lafiya da sauran ayyukan ci-gaba a yankin Arewa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *