Rahotanni na cewa, akalla ma’aikatu da hukumoni 428 na gwamnatin tarayya sun karar da kudin batarwa da aka ware masu a kasafin shekara shekara ta 2020, inda a halin yanzu ma’aikata da-dama ba su samun albashi saboda wannan matsala.

Kason kudin ma’aikatun a asusun IPPIS dai ya kare kar-kaf, kuma ana adana kudin biyan albashi ne a cikin asusun da ke ofishin babban akawun gwamnatin tarayya.

Wani jami’in gwamnatin tarayya da ya zanta da ‘yan jarida a boye, ya ce abin mamaki ne kudin biyan albashi su kare kafin karshen shekara.

Jami’in, ya ce dole shugabannin hukumomin da matsalar ta shafa su yi bayanin ainihin abin da ya faru da kudin da aka ware masu a farkon shekarar nan.

Yayin da ma’aikatan gwamnatin tarayya ke fama da rashin albashi, rahotanni sun nuna cewa kamfanin NNPC ya kashe Naira biliyan 375 wajen biyan albashi a shekarar da ta gabata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *