Dangin fursunoni dubu 1 da 181 daga cikin wadanda su ka gudu daga gidajen gyaran hali na Oko da ke Benin, sun maida su da kan su kamar yadda rahotanni su ka ruwaito.

Wata majiya ta tabbatar da cewa, ‘yan’uwan mutane 24 daga cikin wadanda su ka gudu sun maida su tare da lauyoyin su bisa umarnin gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki.

Tun farko dai gwamnan ya umarce su da su yi gaugawar komawa ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.

Idan dai ba a manta ba, bata-gari sun yi amfani da damar zanga-zangar EndSARS wajen kai wa gidajen yari da ke jihar hari su ka saki fursunonin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *