Tsohon Shugaban Hukumar Tara Kudaden Haraji na Cikin Gida Babatunde Fowler, ya bayyana ofishin Hukumar EFCC.

Kakakin Yada Labarai na hukumar EFCC Wilson Uwujaren ya tabbatar wa manema labarai cewa, gayyatar shi aka yi kuma ya kai kan sa a ofishin na shiyyar Lagos, sai dai bai bayyana dalilan gayyatar ba.

Kafin shugabancin hukumar daga shekara ta 2015 zuwa ta 2019, Fowler ya shugabancin Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Jihar Lagos tsawon shekaru takwas.

Shugaba Buhari ya tura ma shi takardar gargadin sanin dalilin da ya sa hukumar ta kasa tara haraji mai yawa tsawon shekara hudu, ganin cewa tun a shekara ta 2015 a lokacin Jonathan ba a kara tara mai yawa a wata shekara kamar na shekara ta 2015 ba.

A Cikin watan Disamba na shekara ta 2019, shugaba  Buhari ya cire shi ta hanyar kin kara ma shi wa’adi karo na biyu, bayan ya kammala zangon shekaru hudu na farko.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *