Mayakan Boko Haram sun kai hari kauyen Chibok tare da kashe akalla mutane 12.

Wannan ne harin baya-bayan nan da Boko Haram ta kai tare da kungiyar ISWAP, wadda ta fice daga cikin kungiyar ta ke kuma kai hare-haren ta a yankin.

Wani shugaba a yankin Chibok ya shaida wa manema labarai  cewa, maharan sun shiga kauyen Takulasi a motoci dauke da bindigogi kusa da kauyen Chibok, sun kashe ‘yan garin mutane 10 da mutane biyu daga cikin ‘yan sintiri.

Wasu majiyoyi sun ce, maharan sun yi awon gaba da mutane da dama, ciki har da wata mata da ke shayarwa da jaririn ta, sannan  sun kona gidaje da dama, lamarin da ya tilsta wa mutanen kauye tserewa da rayuwar su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *