Helkwatar tsaro ta sojin Nijeriya, ta musanta zargin cewa sojoji sun kashe mutane huɗu a Jihar Filato, yayin da matasa ke ƙoƙarin wawashe gidan tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.

Idan dai ba a manta ba, rahotanni sun ce dakarun rundunar Operation Safe Heaven  sun halaka mutane huɗu, tare da jefa gawarwakin nsu cikin kogi a garin Gwafan da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.

Helkwatar tsaron ta ce, rahoton abin cutarwa ne ga sojojin Nijeriya da kuma Operation Safe Heaven, waɗanda su ka tabbatar da zaman lafiya a Filato.

An dai sha zargin rundunar sojin Nijeriya da kisan masu zanga-zangar EndSars a Lekki Toll Gate da ke Jihar Legas, sai dai sun musanta zargin, su na masu cewa ba su je wajen ba gaba ɗaya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *