Dakarun soji sun kashe sama da ‘yan ta’adda uku, yayin da su ke kokarin kai wa tawagar masu maida ‘yan gudun hijira zuwa garin Baga daga Maiduguri hari.

Kakakin rundunar sojin manjo janar John Enenche, ya ce an kwaci miyagun makamai a hannun su, bayan sun kama wani mai garkuwa da mutane a karamar hukumar Takum da ke jihar Taraba.

Enenche, ya bayyana haka ne a hedkwatar tsaro da ke Abuja, yayin gabatar da jawabi a kan harkar tsaro, inda ya bayyana yadda su ka kama wasu masu garkuwa da mutane da su ka hada da wani Yahaya Mohammed da Juli Ardo a kauyen Zalau da ke kananan hukumomin Toro da Kirfi a jihar Bauchi.

Ya ce yanzu haka wadanda ake zargin su na hannun hukumomi domin fuskantar hukunci.

Enenche, ya ce rundunar Operation Wutar Tafki ta kai hare-haren sama, inda su ka samu nasarar ragargazar maboyar su a kauyen Ngosike da ke kusa da dajin Sambisa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *