Kwamitin da gwamnatin Jihar Legas ta kafa na jin bahasin abin da ya faru a harbe-harben da ake zargin sojoji sun yi yayin zanga-zangar EndSars ya cigaba da zaman sa a rana ta uku.

Kwamitin, ya ziyarci Lekki Toll Gate, a ci-gaba da binciken zargin harbin masu zanga-zangar, inda ‘yan kwamitin su ka ɗebo kwamson harsasai da aka harba kuma su ka ce za a bincike su.

Tuni dai rundunar soji ta musanta zargin, ta na mai cewa dakarunta ba su je wurin kwata-kwata ba.

An dai kafa kwamitocin ne a jihohi domin bincike tare da biyan diyya ga waɗanda ‘ya sanda su ka ci wa zarafi ko kisa ba tare da haƙƙi ba, a matsayin wani ɓangare na biyan buƙatun masu zanga-zangar neman gyara a ayyukan ‘yan sandan Nijeriya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *