Gwamna Nasir El-Rufa’I na jihar Kaduna ya ce shawarar da kwamitin su na jam’iyyar APC ya bada na sauya fasalin Nijeriya ita ce mafita.

Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi, shi ne babban baƙo mai gabatar da jawabi a wajen taron, mai taken ‘Ci-gaba da Nuna Nagarta Zuwa ga Cikakken Haɗin Kai’.

Daga cikin gwamnonin da su ka halarci taron akwai na jihohin Ekiti da Jigawa da Sokoto da Kebbi da, Kaduna, sannan akwai Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubkar.

A wajen taron, Sarkin Musulmi ya gabatar da Alhaji Ali Sarkin Mota, wanda shi ne direban marigayi Sir Ahamdu Bello Sardauna a lokacin da ya ke Firimiyan Arewa ga sauran manyan baƙi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *