An kama ɗan wani tsohon minista bisa zargin yunkurin fashi da makami a wani wurin canjin kuɗi da ke Abuja.

Yanzu haka dai yaron wanda ake zargin ɗan wani tsohon minista ne daga Jihar Benue, ya na tsare ahannun hukuma, inda ake ci-gaba da bincike kamar yadda rahotanni su ka bayyana. #

Wata majiya ta ce, tsohon ɗan ministan ya kutsa wurin canjin kuɗin  cikin motar mahaifin sa ne a makon da ya gabata ɗauke da bindiga don ya yi fashin kudi.

Majiyar ta ce, yayin da ya ke sata a wajen, ɗaya daga cikin masu aiki a wurin ya kama shi, inda yay i ma shi dukan raba-ni-da-yaro kafin ya mika shi a hannun ‘yan sanda.

Binciken farko da aka gudanar ya tabbatar da cewa, wanda ake zargin ma’aikacin hukumar gwamnatin tarayya ne da ya saba da rayuwar almubazaranci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *