Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya ce matukar ana so a shawo kan matsalolin Najeriya, ya zama wajibi a magance talauci da rashin aikin yi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana wajen kaddamar da wani shiri na wayar da kan ‘yan Najeriya miliyan 20 dake da son ganin an inganta harkokin gudanar da mulki.

Tambuwal wanda ya samu wakilcin mai bashi shawara kan harkokin kanana da matsakaitan masana’antu, Akibu Dalhatu, ya ce dole a magance wadannan matsaloli matukar ana so a zauna lafiya.

Ya ce ya zama wajibi a ba bangaren kula da jin dadin al’umma da tsaro muhimmanci, a cewarsa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fito da tsare-tsare da dama wadanda za su taimaka wajen magance matsalolin.

Gwamnan ya ce ba al’umma mihimmanci a cikin tsarin fitar da kasafi zai taimaka wajen sanin irin abubuwan da ya kamata a fara tunkara dake ci musu tuwo a kwarya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *