Kungiyar kwadago ta Najeriya ta bukaci gwamnatoci a dukkanin matakai su kara inganta bangaren lafiya ta yadda za a kawo karshen zuwa neman magani a kasashen ketare.

Shugaban kungiyar na kasa Ayuba Wabba, ya bayyana haka a lokacin da yake magana a wajen wani taro wanda ya gudana a Abuja.

Wabba ya ce bullar cutar korona, ya nuna irin sakaci da aka yi da irin nakasu da Najeriya ke da shi a bangarorin kula da lafiya.

A cewarsa ba Najeriya kadai ba, cutar ta nuna karancin ba bangaren lafiya muhimmanci na kasashe da dama, wanda hakan ya sa rayuwar ‘yan kasashen a cikin hadari.

Wabba ya ce gwamnatocin da suka gabata sun gaza yin abin da ya kamata ga bangeren lafiya, sai dai kawai yada abubuwan da bah aka yake ba a bangeren.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *