Shelkwatar tsaro ta Najeriya ta ce runduna ta musamman dake yaki da ayyukan ta’addanci da aka yiwa lakabi da Operation Fire Ball, ta kasha ‘yan ta’addan Boko Haram 22 a wani hari da ta kai Damboa dake jihar Borno.

Mai rikon mukamin jami’in yada labarai na tsaro Birgadiya Janar Benard Onyeuko, ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Ya ce ‘yan ta’addan sun so su kai hari ne a sansanin soji dake Damboa, inda jami’an sojin suka yi gaggawar daukar matakin kariya akan hakan.

Onyeuko ya ce wannan na zuwa ne bayan kafa sabuwar rundunar karkashin rundunar Operation Lafiya Dole.

Ya kara da cewa jami’an sojin sun kai harin ne a ranar 25 ga wannan watan, tare da goyon bayan hare-hare ta sama, kuma sun yi nasarar lalata kayayyakin yaki da ‘yan ta’addan da dama, tare da kwato wasu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *