Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya NCC ta ce ta sanya sama da naira billiyan dari 3 da 44 a asusun gwamnatin tarayya a cikin shekaru 5 da suka gabata.

Mataimakin shugaban hukumar Umar Danbatta ya bayyana haka, a lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin kula da harkokin sadarwa na majalisar wakilai karkashin jagorancin Akeem Adeyemi.

Daraktan kula da sashen yada labarai na hukumar Ikechukwu Adinde, ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Adinde ya ce Danbatta ya yi amfani da kyakyawar alakar dake tsakanin hukumar da majalisar dokokin wajen fada musu irin nasarori da hukumar ta samu.

Ya ce bangaren sadarwa ya bada sama da kashi cikin dari na tattalin arziki a shekarar 2015, yayin da a watanni 4 na tsakiyan wannan shekarar ta bada gudunmawar sama da kashi 14 cikin dari.

A nasa jawabin Adeyemi ya ce makasudin ziyarar ta su shine domin sanya ido, kamar yadda kundin tsari na 1999 ya tanada.

Sannan ya yabawa shugabannin hukumar bisa yadda suke gudanar da tsare-tsare cikin fili, tare da gaskiya da adalci, da kuma fito da wasu tsare-tsare da za su taimakawa tattalin arziki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *