Gwamnatin tarayya ta ce za ta yi dukkanin mai yiwuwa dan ganin tsohuwar ministar kudi Ngozi Okonjo-Iweala ta shugaban cibiyar cinikayya ta duniya duk da adawa da hakan da kasar Amurka ke yi.

Ma’aikatar kula da harkokin kasashen ketare ta bayyana haka ta bakin jami’in yada labarai da hulda da jama’a Ferdinand Nwonye.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da ganin Okonjo-Iweala, ta kai ga nasara, domin a cewarsa nasarar ta nasara ce ga Najeriya baki daya.

Nwonye ya ce baya ga cin zaben, akwai bukatar kasashen da ke cikin cibiyar su daidaita tare da tsaida wanda ya kamata ya zama shugaban cibiyar, kuma ita tafi cancanta.

Ya ce an cimma matsaya kan gudanar da taron masu ruwa da tsaki na cibiyar za su gana domin cimma matsaya ta karshe akan shugabancin cibiyar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *