Fadar shugaban kasa ta ce gwamnatin tarayya ba za ta kafa wani kwamiti na musamman da zai binciki zargin da ake yiwa sojoji na harbin masu zanga-zangar adawa da rundunar SARS a Lekki dake jihar Legas ba.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Femi Adesina ya bayyana haka a lokacin da yake magana a wani shiri na kafar talabijin.

Ya ce ba inda kundin tsarin mulki ya ba shugaban kasa Muhammad Buhari damar gudanar da irin wannan binciken, balle har a kafa kwamiti na musamman.

Ya ce kundin tsarin mulki da aka yiwa kwaskwarima na 1999, ya ba shugaban kasa ikon gudanar da irin wannan binciken ne kawai a babban birnin tarayya Abuja.

Tuni dai gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya kafa kwamitin shari’a na mutane 7 da zasu gudanar da cikakken bincike na zargin jami’an ‘yan sanda da cin zarafin al’umma.

Kwamitin karkashin jagorancin mai shari’a Doris Okuwobi, inda ya gudanar da zaman san a farko a ranar Talatar da ta gabata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *