Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya bada tallafin karatu marayun da aka kashe iyayen su a fagen daga yayin yaki da mayakan Boko Haram a cikin shekaru bakwai da su ka gabata.

Bayan daukar nauyin karatun yara, Zulum ya kuma bada da tallafin jin-kai na Naira miliyan 180 ga matan da aka kashe mazajen su a fagen daga, inda kowaccen su ta samu naira dubu 50, tare da rarraba buhunan kayan abinci dubu 27 ga ‘yan kato da gora kimanin dubu 9.

Gwamnan ya sanar da daukar mataki da bada tallafin ne yayin wani biki da aka gudanar a harabar jami’ar Maiduguri.

Ko wane daya daga cikin mayakan sa-kai da ke taimaka wa sojoji yaki da Boko Haram ya samu tsabar kudi naira dubu 20, da buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50, da katon na Taliyar Spaghetti da kuma galan na man girki, baya ga alawus da su ke samu na wata-wata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *