Shugaba kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci ‘yan Nijeriya su yi amfani da bikin Maulidi wajen koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammadu (SAW) ta hanyar nuna kauna da fahimta ga juna.

Buhari ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya su yi koyi da kyawawan halayen Annabin tsira na hakuri da gaskiya da rikon amana da mutunta kowa.

Da ya ke misali da yawan rikice-rikice da sace-sacen da aka fuskanta bayan wasu bata-gari sun janye zanga-zangar EndSARS, Buhari ya bukaci matasan Nijeriya su yi watsi da duk wasu munanan halaye.

Shugaba Buhari, ya sha alwashin tabbatar da hukunta duk wadanda ke da hannu a sace-sacen kayayyakin gwamnati da na mutane masu zaman kan su.

Dangane da annobar korona, Shugaba Buhari ya ce ya zuwa yanzu Nijeriya ta yi nasarar magance matsalar ta hanyar tabbatar da adadin mutanen da su ka kamu da ita ya yi kasa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *