Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya maida Salihu Tanko Yakassai da aka fi sani da Dawisu bakin aikin sa na mai taimaka ma shi ta fuskar yada labarai.

Ganduje ya yi hakan ne, makonni biyu bayan dakatar da shi daga mukamin sa saboda sukar shugaba Buhari da ya yi a shafin sa na Tuwita.

Salihu Tanko Yakassai ya bayyana haka ne a shafin sa na Twitter, inda ya mika godiyar sa ga jama’ar da su ka taya shi farin cikin komawa bakin aiki.

Ya ce ya na mika godiya ga duk wadanda su ka kira ko su ka tura sakonnin taya shi murnar komawa aiki bayan Ganduje ya dakatar da shi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *