Babban Bankin Nijeriya CBN, ya fitar da tsarin yadda za a tallafa wa matasa da jari a karkashin shirin gwamnatin taraya da ta ware naira biliyan 75 domin tallafa wa matasa.

Bankin ya fara fitar da kason farko na naira biliyan 12 da rabi daga cikin kuɗin domin bunƙasa matasa, sannan ya bayyana ƙaramin bankin NIRSAL da ke ƙarkshin sa a matsayin wanda zai tafiyar da shirin.

Gwamnatin tarayya, ta ce shirin ya shafi sama wa matasa dubu 500 ayyukan yi, waɗanda za su amfana da shirin duk shekara tsakanin 2020 zuwa 2023.

Tsarin dai ya shafi matasa ‘yan tsakanin shekaru 18 zuwa 35 da gwamnati za ta tallafa mawa, waɗanda ke da tunanin kasuwanci

Bankin, ya bayyana a shafin sa na yanar gizo cewa tsarin tallafin zai dogara ne a tsarin kasuwancin mutum, inda zai iya samu bashin naira dubu 250 na jari.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *