Gwamnatin Amurka, ta ce tsohuwar ministar kudi ta Nijeriya Ngozi Okonjo-Iweala, ba ta da kwarewar da za ta iya jagorancin Hukumar Kasuwanci ta Duniya.

Amurka wadda ta bayyana adawa da takarar Okonjo-Iweala, ta ce ta na goyon bayan ministar kasuwancin Koriya ta Kudu Yoo Myung-hee, saboda ta kware wajen harkokin kasuwanci bayan kwashe shekaru 25 ta na aiki a bangaren da ya shafi manufofin kasuwanci.

A wata Sanarwa da Jakadan Kasuwancin Amurka a Hukumar ya gabatar, ta ce Myung-hee na da kwarewar da za ta iya jagorancin hukumar a wannan lokaci da ake fuskantar matsalolin kasuwanci da dama tsakanin kasashe da nahiyoyi.

Amurka, ta ce Hukumar Kasuwancin na matukar bukatar garambawul domin sake fasalin ayyukan ta, ganin yadda aka kwashe shekaru 25 ba tare da amincewa da sabbin kudaden fito da yadda kasashe ke rikici a tsakanin su ba.

Tuni dai Ngozi ta samu goyan bayan kasashen ECOWAS da na tarayyar Turai da wasu kasashe da ke Asia, wadanda su ka kai wakilai 164 da ke cikin Hukumar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *